23 Faburairu 2022 - 13:36
Kwamitin Tsaron MDD Na Kebabben Zama Game Da Batun Mali

Kwamitin tsaron MDD, na wani kebabben zama yau Talata, domin tattauna halin da ake ciki a Mali, tun bayan da faransa da kawayenta suka yunkuri anniyar janje dakarunsu daga kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Taron wanda faransa ta kira, yayinsa za’a tattauna tasirin janyewar dakarun a kasar ta mali, musaman kan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Mali (Minusma).

Babban abunda damuwar da ake da ita shi ne makomar tawagar ta MINISMA, wacce ta dogara da tallafin dakarun na faransa.

A cewar jami'an diflomasiyya, janyewar Faransa na iya sa tawagar Turai da ke cikin Minusma, kamar na Jamus Burtaniya suma su janye.

342/